Jagoran Jam’iya mai mulki APC Asiwaju Bola Tinubu ya ga na da Dan Takarar Shugaban kasa a inuwar jam’iyar PDP Alh Atiku Abubakar.
Yan siyasan biyu sunyi kwarya kwaryar ganawar ne a filin Jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja.
Mai magana da yawun Tinubu Mr Tunde Rahman shine ya yada hotunan ganawar a shafin sa na sada zumunta Facebook a jiya.
Hotunan na nuni da yadda Mutane biyun ke Tattaunawa a bangare guda kuma gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri yana saurarensu, sai dai ba’a bayyana abi da suka tattauna ba a ganawar.