Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta cimma matsayar zaben tsohon Dan wasanta Mikel Arteta a matsayin Wanda zai karbi ragamar horar da kungiyar.
Rahotanni daga sky sport ta rawaito cewa tuni wakilan suka sukayi tattaki zuwa gidan Arteta inda suka tattauna dashi don karbar matsayin mai horar da kungiyar.
Wakilan sun je ne Jim kadan bayan kammala wasan da aka buga a ranar Lahadi tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester city da Arsenal inda aka lallasa Arsenal da 3-0.
.yanzu haka dai Arteta shine Mataimakin mai horar da kungiyar Manchester city Pep Guardiola.