Wata babbar kotu ta kori karar da ake tuhumar gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da laifin karbar cin hanci da rashawa saboda rashin gamsassun Hujjoji.

Tun a shekarar 2018 ne wata Jaridar Daily Nigerian dake yada labaran ta a yanar Gizo ta wallafa wani faifan bidiyo dake nuna gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na karbar cin hanci a hannun wasu Yan kwangila.
Wani lauya mai zaman kansa Bulama Bukarti ne ya shigar da karar gaban kotu inda ya bukaci kotu ta bawa hukumar EFCC damar bincikar gwamnan akan karbar cin hanci daga hannun yan kwangila.

Gwamnatin jihar Kano ta zargi Editan Jaridar Daily Nigerian Jafar Jafar da yunkurin bata mata suna ta hanyar wallafa faifan bidiyon da bashi da sahihanci.
