Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a yau Laraba, ya saka hannu a kan ƙunshin kasafin kuɗin shekarar 2020.

Gwamna Gandue ya karɓi kasafin ne bayan ya gabatar da shi a majalisa wanda ta duba kuma ta sahale a bisa ayyukan da kasafin ya ƙunsa.

Kasanfin dai ya kai tsabar kuɗi fiye da naira biliyan, wato 206,267,759,657.

Ana sa ran tsarin kasafin zai koma daga farkon kowacce shekara zuwa ƙarshen shekara, wato watan Janairu zuwa watan kowacce Disamba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: