Wasu Yan binding da ba’a San ko suwaye ba sun sace Wani mai rike da sarautar gargajiya a jihar kaduna

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na rana inda wasu yan bindiga dauke da muggan makamai suka shigo garin na Birnin Gwari dake kaduna inda sukayi garkuwa da Alhaji Yusuf Yahaya Mai Dubu (sarkin kudun birnin gwari) da sakataren ilimi na karamar hukumar birnin gwari

Majiyarmu ta Muryar Yanci ta rawaito cewa yanzu haka daya daga cikin wanda akayi garkuwan dasu mai suna Alhaji Magaji Umar jagoran birnin gwari ya arce amman haryanzu shima ba a ganshi ba.
saidai wata majiyar tace a yanzu haka yana hannun jami’an tsaro na yan sanda dake buruku wani kauye dake hanyar kaduna zuwa birnin gwari. Sarkin kudun birnin gwari yusuf yahaya Mai Dubu ya kasance hakimi a masarautar na karamar hukumar birnin Gwari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: