Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani sashen bincike da adana bayanai na musamman a babbar helkwatar rundunar yan sanda da ke Abuja.

Muhammadu buhari ya kuma kaddamar da motoci 139 da na urar daukar hoton sirri 46,, shugaban ya yabawa jami an yan sanda da suke aiki don dakile ayyukan bata gari a fadin kasar

Ya kuma kara karfafa kwarin gwiwa ga jami an yan sandan don samar da tsaro tare da kare rayuka, lafiya da dukiyoyin al ummar Najeriya

A nasa bangaren shugaban ƴann sandan Najeriya Muhammed Adamu yace ababen hawan da aka tanada za suna sintiri ne a babbar hanyar Abuja zuwa kaduna da sauran manyan hanyoyin kasar nan don tababbatar da tsaro a hanyoyin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: