Jami an hukumar hana fasa kwauri ta kasa reshen jihar Adamawa da Taraba ta kwace shikafa mai tarin yawa da aka shigo da ita daga kasashen ketare a wata babbar kasuwa da ke mubi
Sannan sun kama wasu kayyayaki da aka haramta shigo da su kasar tare da kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu wajen shigo da shinkafar
Jami an hukumar sun shiga kasuwar ne da misalin 11 na safe kuma suka shiga bincike shaguna da dakunan ajiyar kayayyaki da ke kasuwa,
A cewar kwantirolan da ya jagoranci aikin mista kamardeen olumoh , yace sun samu umarnin hakan daga helkwatarsu da ke Abuja sannan sun yi amfanmi da sashe na 147 na dokar hukumar, kuma shi ya sahale musu shiga lungu da sako dare ko rana don zakulo dukannin kayan da aka shigo da shi ba bisa ƙa ida ba.


