Cikin wasiƙar da suka aike ga gwamnan Kano Abdullahi Ganduje wadda daraktan Ƙungiyar gwamnonin jam iyyar APC a Najeriya Salihu Garba ya sanyawa hannu, ƙungiyar ta sake tabbatar da cewar jihar Kano ce kan gaba a fannin samar da tsaro wanda ake zaman lafiye fiye da sauran jihohi.

Rahotan da aka tattara bayanai a watan Nuwamban da muke ciki, ƙungiyar ta sake jaddada cewar Kano na gaba  da kaso 22 a fannin saman da ingantaccen ilimi, samar da cigaba a fannin lafiya da sauran ababen more rayuwa.

Wannan ne karo na uku da jihar ke lashe kambu bayan ƙididdigar ayyukan da ake yi a tsakanin jihohin da jam iyyar APC ke mulka a jihohin Najeriya.

Jihar da ke marawa Kano baya ita ce legas da kaso 20 sanan jigawa da ta zamto ta uku da kaso 19 a fannin zaman lafiya da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: