Kwamishinan yan sandan jihar kano Cp Habu Sani yayi holan mutane 173 Wanda ake zarginsu da laifuka daban daban.
Cikin nasarrorin da Rundunar yansandan jihar kano a tsakanin 5 ga watan disamba zuwa 23 ga disamban Rundunar ta cafke Wanda ake zarginsu da garkuwa da mutane su 17 da Yan fashi 13, sai barayin shanu 10 da wani mutun daya da ake zarginsa da safarar yawa zuwa kasashen ketare, da mutane 7 da suka kware wajen satar shanu da garkuwa da mutane.
Haka zalika Rundunar tayi nasarar cafke wani Aminu suleiman mai shekaru 29 da Abdulrashid ishaq dan shekaru 32 Yan unguwar tudun murtala a kano an kamo su a jihar Kaduna bayan sunyi garkuwa da wani yaro mai shekaru 11 a kwana hudu Wanda suka birne shi da ransa a wase dake karamar hukumar minjibir a kano.
Rundunar ta kuma yi nasarar cafke wani da ake Kira da Ali Kwara Wanda yayi kaurin suna wajen fashi da makami da garkuwa da mutane Wanda aka kama shi da bindiga kirar AK47 da alburusai guda Tamanin.
An kuma kama wasu guda 7 da suka kware wajen satan tayoyin mota a unguwar sabon garin kano bayan d suka saci tayoyi Dari biyar da saba’in Wanda kudin su ya kai naira Miliyan goma sha biyar.
An kuma yi nasarar cafke barayin Dabobbi da da Yan daba dauke da manyan makamai.
An kuma gano motoci 5 da wani da ya saci mota dauke da man da ake zubawa a Transfoma drum Goma.
Daga karshe Kwamishinan yansandan jihar kano ya godewa Al’ummar jihar kano da suke bada hadin kai wajen kame bata gari da sauran jami’an yansandan da suke aiki ba dare ba rana don ganin an kawar da bata gari a jihar kano, ya kuma yo addu’ar samun dawammamen zaman lafiya a jihar kano da kasa baki days.