Hukumar dake shirya Jarabawar shiga jami’a JAMB zata fara Jarabawar shekarar 2020 daga 14 ga watan maris zuwa 4 ga watan Afrilu 2020.

Magatakardar hukumar ne farfesa Ishaq Olayede shine ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakoncin Kwamishinan ilimin birnin Tarayyar Abuja a jiya Litinin.
Ya kuma tabbatar da cewa babu dalibin da za’a masa Rijista muddin bai mallaki Shaidar katin dan kasa ba.

Kamar yadda Majalisar Tarayya da Majalisar Zartarwa suka bada umarni.

A don haka farfesa Ishaq yayi Kira ga daliban dake Shirin rubuta Jarabawar JAMB dasu tabbata sun mallaki katin su kafin Lokacin Rijista.