Shugaban hukumar dake lura da jami’oin kasar nan NUC Farfesa Abubakar Rasheed yace hukumar ta sallami daya daga cikin ma’akatan ta sakamakon kamashi da laifin karbar cin hanci da Rashawa lokacin da ake tantance wasu jami’oi.

Farfesa Rasheed ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da Yan jaridu a jiya, a birnin Tarayyar Abuja.
A cewarsa tantance jami’oi yana bukatar bin matakai daban daban don tabbatar da ingancin jami’a.

Farfesa yace aikin tantance jami’oi matakai ne masu tsauri hatta Farfesoshin dake aiki a hukumar sai Wayanda suka yi karatunsu a Najeriya ake dauka Wayanda suka San tsarin jamo’in Najeriya.
