Wani Binciken da aka gudanar a Birtaniya ya nuna cewa, yin azumi ko kame baki na zama garkuwa ko kuma riga-kafin wasu cutuka
– Masana sun tabbatar da cewa azumin na tsaftace jini da daidaita sinadarin Insulin wanda hakan ke da matukar amfani ga masu ciwon sukari
A Amurka ne masana suka gano cewa azumi sau biyu a kowanne mako na kara tsawon rai da kariya daga cututtuka.
Masana kimiyya a Amurka sun bayyana cewa, sakamakon wani bincike da suka gudanar, an gano azumi a kowanne mako ko kuma kame baki daga barin cin abinci na wasu awanni a rana na kara tsawon rayuwa tare da zama riga-kafin cututtuka da dama.
Masanan sun ce, azumi sau biyu a kowanne mako na kara tsawon rai da riga-kafi ga garkuwar jiki.
An buga sakamakon wannan binciken ne a mujallar Likitanci ta New England. Ta bayyana cewa cin abinci a cikin awanni 16 zuwa 18 na kowacce rana na kara tsawon rai, rage karfin harbawar jini da riga-kafin cututtuka da dama.