Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, yaja kunnen masu rike da madafun iko cewa kasar najeriya ka iya fuskantar barazanar karewar dukiyarta, sakamakon yawan bashin da gwamnati ke karbowa.

Obasanjo yayi wannan Kira ne a lokacin da yayayin halarci wani taron addini a birnin Legas, inda ya koka kan yadda Najeriya da kuma wasu kasashen Afrika ke ciwo bashi daga bankin duniya, da asasun lamuni na IMF da sauran hukumomi, Wanda hakan barazana ne ga tattalin arzikinsu.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa kididdiga ta nuna cewa, karshen watan Maris da ya gabata na 2019, adadin bashin da ake bin Najeriya a ketare ya kai dala biliyan 81 da miliyan 274.

Rfi hausa
