Hukumar Hizbah a jihar Kano ta ƙara jaddada dokar nan ta hana cakuɗuwar fasinja maza da mata a babur mai ƙafa uku wato adaidaita sahu.

A yayin zantawarsa da Mujallar Matashiya, mai magana da yawun hukumar Mallam Lawal Fagge ya ce dokar tana nan daram kuma za ta fara aiki ne daga gobe ɗaya ga watan janairun 2020.

Ya ce hukumar ta yi wani zama da ƙungiyoyin masu adaidaita sahun kuma suka cimma yarjejeniyar cewa ƙungiyar za ta fara yin wani hoɓɓasa a kan dokar kafin hukumar ta shiga kame waɗanda suka yi kunnen ƙashi.

“Mun yi zama da ƙunyiyoyin masu adaidaita sahu, kuma sun kawo mana roƙonsu sannan kuma dama ko wa azi mutum zai yi akwai hanyoyi daban daban tunda masalaha ma na daga cikin hanyoyin isar da saƙo don haka muka dakatar da zuba dakarunmu don kama waɗanda suka karya wannan doka” a cewar mai magana da yawun hukumar.

Ya ƙara tabbatar da cewar dokar fa tana nan daram kuma za ta fara aiki ne daga gobe 1 ga watan Janairun sabuwar shekara miladiyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: