Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada aniyarsa ta tsame miliyoyin matasa da ke fama da talauci a kasar.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a yayin jawabinsa na sabuwar shekarar miladiyaya ta 2020.
Cikin jawabinsa ya ce ma aikatan najeriya za su samu albashin da zai wadacesu sannan kuma zai maida hankali a fannin tsaro don tabbatar da cikar burimnsa da alkawarin samar da ingantaccen tsaro wanda ya dauka tun a zangon mulkinsa na farko.
Haka kuma shugaban y ace ba zai sake tsayawa takara a karo na uku ba kamar yadda ake yada jita jitar hakan, haka kuma y ace yana nan a kan bakansa don yaki da cin hanci da rashawa.


