Hukumar Hizbah a jihar Zamfara ta kama wani jami in dan sanda tare da wasu mata uku a wani dakin otel da ke birnin gusau.
Kwamandan hukumar dakta Atiku Zawiyya ne ya shaida hakan yayin da yake holen masu aikata laifuka daban daban a helkwatar hukumar.
Ya ce cikin mutane da suka kama akwai wani jami in dan sanda da suka sameshi a wani dakin otel tare da wasu mata uku suna aikata abinda ya sabawa shari a.
Daya daga cikin mata ukun da aka samesu a tare yar asalin jihar Kaduna sauran kuma yan jihar Zamfara ne.
Kwamandan yace sun ja kunnen masu otel din amma suka karya ka ida da dokokin da suka gindaya musu.
Kuma za su gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu da zarar sun kamala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: