Kaji na da buƙatar yanayin sanyi kuma sun fi yin kwai manya tare da samun riba mai yawa a tare da su.

Wani masani kuma mai kiwon kaji a jihar Kano Alhaji Muhammad Aminu Adamu ya bayyana cewar kiwon kaji musamman masu kwai a lokacin sanyi na da riba mai yawa.

Muhammadu Aminu wanda aka fi sani da Abba Boss kuma shugaban rukunin gidajen gonan Nana Farms LTD ya bayyana cewar babu wani ɗar ga waɗanda ke kiwon kajin a yanayi na muku mukun sanyi saboda hanyoyin da suke bi don daidaita yanayin da kajin ke buƙata.

Cikin shirin Abokin Tafiya da ake gabatarwa a Mujallar Matashiya ya ce manoma kaji na amfani ga garwashin wuta don ɗumama ɗakin da ake kiwon kajin wanda ke daidaita yanayin da kajin ke buƙata.

Ya ƙara da cewar manoma kaji sun fi yin asara a yanayin zafi amma lokacin sanyi babu shakka kajin na buƙatar yanayin irinsa wanda idan ya musu yawa ana iya daidaitashi ta hanyar amfani da garwashin wuta don daidaitawa musamman a ƙasa Najeriya.

Kuma kaji masu kwai sun fi yin kwai manya manya a lokacin sanyi.

https://youtu.be/UWVLCqkvhcI

Leave a Reply

%d bloggers like this: