A farkon makon nan ne Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Otunba Adeniyi Adebayo, ya ce, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bai wa ma’aikatarsa umarnin bunkasa tattalin arziki da habaka tattalin arzikin kasar tare da samar da ayyukan yi da bunkasa fitar da kaya waje. Ministan ya fadi haka ne yayin ganawarsa da shugabannin kungiyoyin kwadago guda hudu a Abuja, inda ya ba da tabbacin cewa, ma’aikatar a shirye take ta habbaka tattalin arzikin kasa tare da samar da aikin yi ga matasa.
Ministan Ya kara da cewa, ma’aikatar ta na bayar da gudunmawa cika alkawarin da Buhari ya yi na fitar da mutane miliyan 100 daga talauci a cikin shekaru 10 masu zuwa, ya na mai tabbatar da cewa ma’aikatar ta na aiki kafada da kafada kan wannan shugabanci wajen cimma wannan kudurin Shugaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: