An gano wani dan Najeriya cikin Jirgin Ukraine da sojojin kasar Iran suka harbo a makon jiya.

Dan Najeriya mai suna Dauda Onuraiz wanda Injiniya ne dake aiki a kamfanin Jirgin ta Ukraine na daya daga cikin Wanda suka mutu a sakamakon harbo jirgin nasu sojojin Iran sukayi.
Sai dai kasashen Ukraine da Canada sun bukaci a gurfanar da sojojin da suka harbo jirgin fasinjojin tare da Biyan Diyya ga iyalan mamatan.

Mutane 176 ne suka rasa Rayukansu a harin da ya faru a birnin Tehran, sai dai kasar Iran ta amsa laifinta na cewa harbo jirgin fa sojojinta suka yi sunyi shine bisa kuskure.

Ministan harkokin waje na kasar Iran Javad Zarif ya roki iyalan mamatan tare da neman gafarar jama’a bisa kuskuren da suka aikata na harbo jirgin fasinjan Ukraine.