A yayin ziyarar aiki da mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai jihar Kano a yau, ya yabawa gwamna Ganduje bisa yadda yake ƙoƙari don ayyukan raya ƙasa.

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce Ganduje ya cancanci yabo a bisa yadda yake ƙoƙari don kawar da cutar daji wato kansa ganin yadda ya ɗauki azamar gina cibiyar yaƙi da cutar a jihar.
A cewar mataimakin shugaban ƙasa, hakan ya sa Ganduje ya zama mutum na farko da yake yaƙi da cutar a duk faɗin Najeriya.

A yayin ziyarar tasa ta yau, Fargesa Yemi Osinbajo ya buɗe gadar sama da ke kan titin Murtala Muhammed, da kuma gadar ƙasa da ke ƙofar ruwa, sai wasu manyan ayyuka da ya sa kafin alƙalami ciki har da sabuwar gadar sama da ake ginawa a titin zuwa asibintin murtala da ke ƙofar mata.
