Alƙalin Alƙalan Najeriya ya dakatar da zaman kotun ƙoli don sauraren ƙorafin zaɓen gwamnoni da aka shirya a yau.

Hakan ya biyo bayan rashin lafiyar ɗaya daga cikin alƙalan da ke sauraren shari ar lamarin da ya kawo cikas ga zaman kotun a yau.

Alƙalin Alƙalan Najeriya Justis Tanko Muhammad ya dakatar da zaman na yau kuma a gobe za a cigaba da zaman kotun.

Cikin jihohin da ake shari ar akwai jihar Kano tsakanin Abdullahi Ganduje da Abba Kabir wato Abba Gida-Gida, sai Imo da kuma Sokoto.

Leave a Reply

%d bloggers like this: