Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a Jam iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya bayyana amincewa da hukuncin kotu sai dai ya bayyana yadda aka danni ra ayin al ummar Kano na ƙin basu zaɓinsu.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan PDP ya fitar a yau Sanusi Bature jim kaɗan bayan hukuncin da kotu ta yi kan ƙalubalantar zaɓen da aka yi a shekarar 2019.
“Mun rungumi ƙaddara amma bayan shari’ar duniya akwai wata a lahira” Abba Gida-Gida

Kotu ka bayyana Abdullahi Umar Ganduje na jam iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen, kuma daga bisani ta yi watsi da koken da ɗan takarar jam iyyar PDP Abba Kabir ya yi a kan zaɓen.
