Ɗan takarar gwamnan Kano a inuwar jam iyyar PDP Abba Kabir ya yi watsi da tayin da gwamnan Kano Abdullahi Ganduke ya yi masa na haɗa hannu don tafiyar da gwamnatinsa.

Mai magana da yawun Abba Kabir, Sanusi Bature ne ya bayyanawa kafar yaɗa labarai ta Pyramid FM cewar, ba za su taɓa karɓar tayin da aka yi musu ba kasancewar kowa manufarsa daban.
Ya ce an yi amfani da ƙarfin shari a an danne haƙƙin Al’umma amma sun rungumi hakan a matsayin ƙaddara.

“Ba za mu taɓa haɗa hannu da Ganduje ba tunda mu manufarmu ta al umma ce ahi kuwa tasa kowa ya santa, kuma indai mulki ne a sha daɗi lafiya” Abba gida gida.
