Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi gargaɗi ga masu shirin tada zaune tsaye katin zaɓe da lokacin zaɓe da ma bayan zaɓen da za a sake a wasu ƙananan hukumomi a Kano.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu Ahmadu Sani ne ya yi wannan gargaɗi da bakinsa a yayin da yake wani taron yarjejeniya tsakanin ƴan takarar kowacce jam iyya.

Ya ce rundunar ƴan sandan jihar Kano ta shirya tsaf don tinkarar zaɓen da zai gudana ranar adabar, kuma ba za saka idanu wasu tsirarun mutane su kawo cikas ba, matuƙar kuwa aka samu mutum da hakan to kuwa lallai zai girbi abinda ya shuka.

Taron da ya gudana a ɗakin taro na rundunar da ke Bompai a Kano, ya samu halartar kwamishinan zaɓe na jihar Kano Farfesa Riskuwa Arabu Shehu, da shugaban kula da haɗɗura a ta ƙasa reshen Kano, da kwamandojin sojin sama da na ƙasa da ma shugaban jami an tsaron farin kaya DSS.

Haka kuma ƴan takarkarun da suka halarta na jam iyyar APC da na PDP sun yi alƙawarin bin wannan tsari tare da amincewa rundunar cewar za su ja hankalin magoya bayansu don gujewa faɗawa komar hukumar.

#MujallarMatashiya

Leave a Reply

%d bloggers like this: