Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta saka yau 25 ga watan janairun shekarar 2020 a matsayin ranar da za a gusanar da zaɓen cike gurbin wasu daga cikin ƴan majalisar wakilai ta tarayya da wasu ƴan majalisar dokoki ta jiha.

Mujallar Matashiya ta zagaya wasu daga cikin mazaɓun ƙananan hukumomin Doguwa, Tudun Wada, da Bebeji.
A ƙaramar hukumar Tudun wada mun zagawa mazaɓu da dama inda muka riski jama a na gudanar da zaɓe a wasu wuraren yayinda wasu mazaɓun tuni aka kammala zaɓe a wajen.

Yayin zantawarmu da guda cikin masu yiwa ƙasa hidima da ya buƙaci a sakaye sunansa, ya bayyana mana cewar masu kaɗa ƙuri a ba su fito sosai ba kamar yadda ya ce kashi ɗaya bisa uku ne suka fito a mazaɓar da yayi aikin zaɓen.

A ƙaramar hukumar Doguwa mun zagaya mazaɓu da dama ciki har da mazaɓun da ke cikin garin Daɗin Kowa, Riruwai da sauransu inda a nan ma muka iske mutane na gudanar da harkokinsu da misalin ƙarfe 3 na rana, bayan da muka tuntuɓi wasu daga cikin mazauna garin sun bayyana cewar tun tuni aka kammala zaɓen yayin da kowa ya koma kasuwa don gudanar da harkokinsu, sai dai a mazaɓun ma ba a samu fitowar mutane da yawa ba.
A ƙaramar hukumar bebeji ma haka lamarin yake na rashin fitowar mutane.
A zaɓen da ya gudana a yau an samu wadataccen tsaro kuma babu wani waje da aka samu hargitsi yayin gudanar da zaɓen har aka kammalashi.
Ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun wada dai na da wakili ɗaya a zauren majalisa kamar yadda ƙaramar Hukumar Ƙiru da Bebeji ma ke da wakili a zauren.