Labaran ƙasa
Najeriya zata karbo Bashin Dala Biliyan Daya Don Inganta harkar Noma

Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono,ne ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ciwo bashin dala biliyan Daya domin sawo kayan noma na zamani ta raba wa manoma.

Nanono ya yi wannan bayanin ranar Juma’a a Abuja a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin Shirin Inganta Noma na Green Imperative Programme.
Ya ce za a karbo bashin daga Bankin Kasar Jamus, Da Bankin cigaban Noma na kasar Brazil da kuma Bankin Musulunci, wato Islamic Development Bank.

Ministan ya ce an kulla yarjejeniyar biyan bashin nan da zuwa shekaru 15.

In dai aka karbo bashin dai kamar yadda Nanono ya bayyana, za a sayo kayan aikin noma ne domin a raba wa manoma a fadin kananan hukumomi 774 na fadin kasar nan.
Labaran ƙasa
Mutane Sama Da 7,000 Sun Dawo Najeriya Bayan Tserewa Sakamakon Rikicin Boko Haram

Gwamnatin tarayya a Najeriya ta dawo da mutane 7,790 waɗanda su ka yi gudun hijira sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram.

Hadimin gwamnan jihar Borno Dauda Iliya ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau a Maiduguri
Ya ce gwamnan jihar Babagana Zulum ne ya jagiranci tawagar gwamnatin tarayya don dawo da mutanen da su ka yi hijira zuwa Najeriya.

Sanarwar ta ce an dawo da mutanen ne daga ƙasar Chadi.

Ministan jin kai. Najeriya Dakta Yusuf Sununu na daga cikin waɗanda su ka je wajen
Sai ministan rage talauci Aliyu Ahmed da babban sakatare a hukumar kula da yan gudun hijira
Rahotanni sun ce mafi yawa daga cikin waɗanda su ka yi gudun hijirar ƴan jihar Borno ne.
A cewar gwamna Zulum, waɗanda aka dawo da su iya wadanda au ja nuna sha’awar dawowa ne.
Gwamnatin tarayya ta nuna jin daɗi bisa yadda ƙasar Chadi ta rungumi yan kasar tsawon shekaru.
Labaran ƙasa
Ƙarin Kuɗin Kira Da Na Data Zai Kai Kaso 30 Zuwa 60 A Najeriya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce akwai yiwuwar ƙara kudin kiran waya da data da aika sakonni da kaso 30 zuwa 60.

Ministan sadarwa na ƙasa Dakta Bosun Tijani ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da aka yi da shi a gidan talabiji na Channels.
Ministan ya ce sun karbi rahoto daga masu masana masu zaman kansu kan yadda karin zai kasance

Tun tuni ministan ya yi watsi da bukatar kara kudin da kaso 100 wanda kamfanonin sadarwa su ka bukata.

A cewarsa, za a yi karin kuma ba da jimawa ba amma ba zai kai da kaso 100 ba.
A makon da ya gabata aka fara wani zama da masu ruwa da tsaki kan batun, kuma aka bayar da umarnin nazartar buƙatar haka.
Kamfanonin sadarwa a Najeriya ne dai su ka ce ba za su iya ci gaba da gudanar da ayyukansu ba na tare da sun yi ƙari a kan kudaden kira da data da kuma na aika sakonni ba.
A cewarsu matukar ana buƙatar ingantaccen sadarwa a ƙasa to ya zama wajibi a yi karin kuɗaɗen.
Labaran ƙasa
Babu Ranar Gyara Wutar Lantarkin Arewa – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce babu ranar daina lalacewar wutar lantarki musamman babban layin da ke kai wuta yankin arewa.

Ministan makamashi Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka yayin kare kasafin kudi na shekarar 2025 a gaban kwamitin majalisar dokoki kan makamashi.
Adebayo ya ce sakamakon rashin tsaro ya sa gwamnatin tarayya ba za ta iya tabbatar da ranar daina lalacewar wutar yankin arewa da kuma gyarawa ba.

A cewarsa, babban layin Kaduna zuwa Shiroro zu a Mando shi ne layi na biyu mafi girma da ke kai wutar lantarki arewa, kuma har yanzu ba a gyara ba saboda rashin tsaro.

A sakamakon rashin gyaran ne ya sa sauran layikan ke ci gaba da faduwa.
Ya ce a yanzu za a ci gaba da fuskantar yawan faduwar layukan wutar.
Ministan ya ce hadin gwiwar da su ka yi da ofishin mashawarcin shugaban kasa kan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu bai kawo karshen kalubalen da bangaren ke fuskanta ba.
Ministan ya ce su na shirin saka kyamarorin tsaro da fitilu masu amfani da hasken rana a wuraren da hanyoyin layin lantarki ya ketara domin magance matsalar a gaba.
-
Labarai1 year ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare6 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada6 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai6 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini5 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari6 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari