Gwamnatin jihar kaduna ta bada umarnin iyaye su kai yayansu makaranta ko su fuskanci hukuncin Kuliya.
Babbar sakatariyar ilimin jihar Mrs Phoebe yay ice ta bayyana hakan a lokacin da take ganawa da take tattaunawa da kamfanin dillancin labarai ta kasa.
Phoebe tace kowane da yana da yancin a bashi ilimi matakin farko kuma dole, don haka gwamnatinsu ta dauki gabarar tabbatar da hakan.
Ta kuma kara da cewa wannan mataki da gwamnati ta dauka yana cikin shirin gwamnati na tabbatar da kowane gida a jihar akwai masu ilimi kuma ingantacce, don haka iyaye basu da wani uzuri da zasu bayar na kin tura yayansu makaranta kasancewar Gwamnati ta dauke duk wasu dawainiya da zasuyi na kudi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: