KETARE
Lauyoyin fadar shugaban white house karkashin jagorancin Pat Cipollone sun soma gabatar da hujjojin wanke shugaban kasar Amurka Donld Trump a zauren majalisar dattijai bisa zargen zargen da ake masa na aikata laifukan da suka bada damar tsigeshi.
Zarge zargen dai sun hada da hana majalisar gudanar da ayyukanta kan binciken zargin Neman kasar Ukraine tayi katsalandan cikin zaben Amurka ta hanyar bada sunan Joe Biden babban abokin hamayyara Trump.
Tuni dai yan majalisar wakilai da yan Democrat suka fi rinjaye sun kada kuri’ar tsige Donald Trump tun a ranar 18 ga watan disamban 2019,
Sai dai majalisar Dattajai mai rinajayen yan jam’iayr Republican mai mulki zasu kada kuria don ganin makomar Donald Trump .


