Sabon mataimakin sufeton ƴan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta ɗaya Sadiƙ A Bello ya ziyarci kwamishinan ƴan sandan jihar Kano a hwlkwatar da ke Bompai.

A yayin ziyarar da ta tattara manyan jami an ƴan sanda jihar ya samu tarba bisa jagorancin kwamishinan ƴan sandan jihar Habu A Sani.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu A Sani ya bayyana masa irin nasarorin da aka samu tun bayan da ya zama kwamiahina a Kano.

Haka kuma ya bayyana masa manyan abubuwan da jihar ta ƙunsa a ziyarar da ya kai don samun bayanan yadda ayyuka ke gudana.

Sannan ya jinjinawa sufeton ƴan sandan Najeriya bisa yadda ya bawa ƴan sanda dama don yaƙi da ɓata gari tare da tabbatar da samar da tsaron lafiya da rayuka da ma dukiyoyin al umma.

Sabon mataimakin sufeton ƴan sandan Sdiƙ A Bello ya jinjinawa kwamishinan bisa yadda yayi ƙoƙarin kame waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban daban a faɗin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: