Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ciwo bashin naira biliyan 15 don gudanar da tsarin ilimi kyauta a Kano.

Shugaban majalisar Abdullahi Garba Gafasa ne ya bayyana hakan yau Laraba bayan mataimakin shugaban masu rinjiye ga bayar da rahotonsa.

Za a ciwo bashin daga bankin GTBank kuma ana sa ran za a biya cikin watanni 30.

Ana sa ran ƙananan hukumomi 44 da ke Kano za su samu fiye da naira miliyan 300 don gudanar da tsarin.

Gwamnatin jihar Kano ce yi alƙawarin bayar da ilimi kyauta kuma dole a jihar, har ma wasu suka ɗauki salon hakan daga magwaɓtan jihohi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: