Alamu sun fara nuna cewar sabon dan majalisar Kiru da bebeji Wanda yayi nasara a zaben cike gurbin da ya gabata a makon jiya na shirin komowa jam’iyyar APC mai mulki.

Datti-Yako ya samu ƙuri’a 48,601, yayinda tsohon dan majalisa Abdulmuminu Jibrin-Kofa ya samu ƙuri’u 13,507.

Wasu majiyoyin sun bayyana cewa shugabannin APC a jihar sun kammala shiri da Datti-Yako na ya koma jam’iyya mai mulki bayan ya ci zaɓe.

A wani yanayi na tabbatar da wannan jita-jita, kwana biyu da bayyana Datti-Yako a matsayin wanda ya lashe zaɓen, an ga sabon ɗan majalisar a hotuna daban-daban yana riƙe da Takardar Shaidar Cin Zaɓensa da shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas.

Wasu hotunan kuma sun nuna Datti-Yako yana gaisawa da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, abinda ke nuna ya yi watsi da PDP, ya koma APC.

Madogara
Muryar yanci

Leave a Reply

%d bloggers like this: