Mai ba gwamna shawara a kan walwalar ƙananan yara a jihar Kano Hajiya Fatima Dala ta gana da kwamishinan ƴan sanda kan yadda za a shawo kan matsalar da ake fama da ita.

A yayin wata ziyara da ta kai helkwatar ƴan sanda da ke Bompai, Hajiya Fatima Dala ta nemi haɗin kan ƴan sanda don kwatowa yara ƴanci a Kano tare da magance fitintunin da suka shafi yara a Kano.
Ta ce yara ne manyan gobe kuma sune shugabanni don haka ba abu ne na wasa ba dole sai an haɗa kai da ƴan sanda don kyautata rayuwarsu.

Kwamishinan ƴan sandan Kano Habu Ahmadu Sani ya yi alƙawari bada dukkanin gudunmawa da ake buƙata daga ɓangaren ƴan sanda don samun nasarar aikin ofishinta.

Yayin da yake bayani a kan batun, ya ce abu ne mai muhimmancin gaske kuma a shirye suke don ƙara ƙarfin gwiwar tafiyar.