shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana haramta wa yan Najeriya da wasu kasashe 5 shiga kasar.

Trump ya bayyana hakan ne a jiya jama’a.

Bayan Najeriya harda kasashe biyar da suka hada da : Myanmar, Eritrea, Kyrgyzstan, Sudan da Tanzania.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin Amurka ta fitar ta ce wannan mataki ya biyo bayan rashin hadin kai daga kasashen da abin ya shafa tare da rashin samun bayanan, tsaron kasa da sauransu.

Tun a wurin taron tattalin arzikin da ya gudana a birnin Davos shugaba Trump ya sanar da aniyarsa ta kara yawan kasashen da zai haramta musu shiga Amurka, ciki harda Najeriya.

Idan ba’a manta ba tun a lokacin yakin zabensa Trump ya sha bayyana cewa zai haramta wa Musulmai shiga Amurka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: