Shugaban gidan gonar NANA Farms Alhaji Muhammad Aminu Adamu da mutane ke kira Abba Boss ya ce ko yanzu abubuwa sun fara sauƙi ssanadin rufe iyakokin Najeriya.

Abba Boss ya bayyana hakan ne a yayin da ake hira da shi a wani shiri mai suna Abokin Tafiya da Mujallar Matashiya ke yi duk wata.

Ya ce za a samu ƙarin sauƙin abubuwa sosai tunda ƴan ƙasa sun fara dogaro da abubuwan da ake samarwa a cikin gida kuma ya fara wadata.

Ya ce a nan gaba ma zai zamto Najeriya na fitar da abubuwan da ake samarwa zuwa ƙasashen ƙetare na daga ci da sauransu.

Ya bayyana cewar idan aka yi la akari da lokacin da aka rufe iyakokin Najeriya zuwa yanzu, a ɓangaren manoma kaji, ana ganin kaji da kwai da ake samarwa sun yi ƙaranci har ma suka yi tsada wanda a yanzu farashin ke daidaita yana sakkowa ƙasa.

Sannan ya ja hankalin ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri don cin galabar kyakkyawar manufar da ke tattare da hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: