Mai ɗakin gwamnan jihar Kano hajiya Hafsat Abdullahi Ganduje ta ce akwai rawar da mata za su taka a cikin gwamnati don kawo cigaba.

Hajiya Hafsat da ta samu wakilcin Dakta Mariya Mahmud kwamishiniyar Ilimin gaba da sakandire ta yi wannan jawabi ne jim kaɗan bayan kammala bata lambar yabo da ƙungiyar ɗaliban arabiyya mata a makarantar Gwauron dutse suka bata don miƙa godiya da bawa ƴaƴan ƙungiyar muƙami a gwamnati.

Ta ce tana fata hakan ya ɗore domin samun mutane maau hazaƙa zai taimaka wajen tafiyar da gwamnati.

Cikin mutanen da aka bawa muƙami a makarantar aji na shekara ta 89, akqai Dakta Zahra u Umar kwamishiniyar mata a jihar Kano sai Dakta Halima sakatariya a hukumar lura da ilimin manya a jihar Kano.

Dakta Zahra u ta yi jawabin godiya tare da kira ga sauran ɗalibai da au kasance masu hazaƙa don kaiwa matakin da ba su taɓa tsammani ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: