Jakadan Al’ummar kasar Chana a Najeriya Mr Zhou Pingjan ya ce ofishin jakadancin Chana ta Dakatar da bada Shaidar shiga Kasar.
Ofishin jakadancin ta dau wannan Mataki ne don kiyaye lafiyar Al’ummar Najeriya da sauran kasashe.
Mr Zhou yace wannan Mataki zai taimaka wajen kiyaye lafiyar Al’umma duniya ba na Yan kasar Chana kawai ba.
A cewarsa wannan cuta ta Corona Virus na dada yaduwa a sassan kasahen duniya don haka suka dauki Matakin dakile shi a Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewa Gwamnati na shawartar Al’ummar Najeriya Dake Shirin tafiya zuwa kasar Chana da su janye Shirin don kiyaye lafiyarsu da ta Al’ummar kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: