Tare da Fatima Abdulhadi Hotoro

Hukumar Hana Fasa Kauri ta Najeriya, (Custom) tayi nasarar kama wasu makudan kudade
sama da Dala miliyan 8 a filin tashi da saukan jiragen sama na kasa dake jihar legas.

Shugaban Kwastam, Hamid Ali ya ne
bayyana cafke kudaden a lokacin da yake ganawa damanema labarai inda yace.
An cafke makudan kudaden ne a cikin wata mota a daidai lokacin da ake
shirin loda su cikin jirgin sama don tsallakawa dasu kasashen ketare.

Haka zalika yace motar da aka zuba kudin aciki. mallakar Hukumar Kula da Kayayyakin Jiragen Sama ta Najeriya (NAHCO)ce.

Yanzu haka dai Tuni aka cafke direban motar da kuma wani ma’aikacin Hukumar ta NAHCO
Kan zargin su da hannu a yunkurin sama da fadi da dukiyar kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: