Tare da Sunusi Rabi’u katsina
Kungiyar Alherin dadin kowa dake karkashin gidan talabijin na arewa24 ta kai ziyara ta musamman ga kwamishinan ma’aikatar yada Labarai da al’adu na jiha katsina a ranar litinin da ta gabata.
Ziyara na nufin hada gwuiwa da ma’aikata karkashin jagoranci shugaban kungiyar Malam Sulaiman Mainasara Kanika da akafi sani da malam Kabir Makaho a shirin da suke gabatar wa na dadin kowa.
A jawabin maraba da tayi babbar sakatariyar ma’aikatar yada labarun Hajiya Dr Talatu Nasir, ta yi matukar murna da wannan ziyara ta hada gwuiwa dan wayar ma da al’umma kai ga me da illar shiga harkokin garkuwa da mutane.
Shima anasa jawabin kwamishinan yada labarai Alh Abdulkarim Yahaya Sirika. ya nuna godiyar shi da wannan kuduri na su, kuma ya yi alkawarin bada goyon baya dan acigaba da nuna wadannan ayuka dan fadakarwa kan illolin garkuwa a jihar katsina da ma kasa Baki daya.
Kwamishinan ya kuma bukaci al’umma da su zama ma su taimakama jami’an tsaro dan ba gwamnati kadai ke da hakkin kare jama’a ba, har ma da mu kan mu muhadu mu magance matsalar da ke cimana tuwo a kwarya.
Tun farko a jawabin shugaban kungiyar ta alherin dadin kowa malam Sulaiman Mainasara da sakataren sa sun bayyana cewa jihar katsina ne gida shiyasa za su fara gudanar da wannan shirin fadakarwa a jihar.