Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta shirya liyafar karrama AIG Ahmed Ilyasu

Bisa jagorancin kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu Ahmadu sani, rundunar ta ahirya liyafa ta musamman don karrama tsohon kwamishinan ƴan sandan Kano.

Taron wanda ya gudana a ɗakin taro na runduna ƴan sanda da ke unguwar Bompai, kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayyana AIG Ahmed Ilyasu a matsayin mutum jajirtacce mai ƙoƙarin samar da zaman lafiya a aikinsa.

Tsohon kwamishinan ƴan samdan Kano Ahmed Ilyasu da ya samu ƙarin girma zuwa mataimakin sufeton ƴan sandan Najeriya shiyya ta biyu a jihar legas, ya bayyana cewar haɗin kan Al umma ne ya bashi dukkan nasarar da ya samu.

Ya miƙa godiya ga rundunar ƴan sandan Kano sannan ya ce, gaskiya da yin aiki tuƙuru saboda Allah shi ya bashi damar da yake kai a yanzu.

Taron dai ya samu halartar da yawa daga cikin ƴan sanda ciki har da rakiyar ƴan ƙabilar Igbo da Yarabawa tare da wasu daga cikin masu riƙe da sarautar gargajiya da ke Zariya.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: