Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran jiha

Anyi kira ga Yan jaridu da su kasance jakadu nagari a tsakanin Al’umma

Tare da Sunusi Rabi’u katsina

Wannan kiran ya fito ne ta bakin sabon shugaban kungiyar ‘yan jarida na kasa reshen jihar katsina kwamared Tukur Hassan Dan Ali.

Shugaban ya bayyana cewa tun farko da yana yakin neman zabe ya bayyana cewa zai dora daga inda suka tsaya da tsohon shugaban kungiyar wato kwamared Buhari Mamman Daura.

Alh. Tukur Dan Ali wanda a baya shi ne Sakataren wannan kungiyar, ya kara bayyana cewa zuwan su a baya sun samu nasarar gyare gyaren wannan sakatariya ta Yan jarida sabanin baya lokacin da su ka karbe ta ba haka ta ke ba.

Haka kuma ya kara tabbatar da cewa a zuwan su da tsohon shugaban ne suka samu nasarar gina shaguna bakin sakatariyar dan samun kudin Shiga tare da gyaran dakin taro wanda shi ma a yanzu haka ya ke tallafama kungiyar ta hanyar yin taruka da shirye shirye.

Sannan akwai karin nasarar karrama wa su daga cikin fitattun mutane da suma tsofaffun yan jarida ne da ba’asaniba, kamar su wazirin katsina Sani Lugga, Marigayi Isah Kaita, Marigayi Shehu Musa Yar Adua, da irin Wada Maida da dai sauran su.

Cikin kudirin mu acewar Shugaban akwai bukatar gyaran tafiyar da aikin jarida ta fuskar da’a da tayi karanci a idon kanana zuwa manya, sannan kuma ta wannan fuskar ne zakaga babi girmamawa kuma baka tantance babba ko karami to shi ma muna kokarin daidaitawa.

Sannan na cikin kudurin yaki da Yan jaridar bogi, kuma cikin ikon Allah makon da ya gabata mukai nasarar wa ni Dan jaridar bogi kuma mun damkama jami’an tsaro shi tare da daukar ma shi matakin da ya dace, kuma za mu cigaba da kula da sa ido.

Haka zalika muna bin dukkan abin da tsarin da dokar aikin jarida ta bayar da shi mu ke amfani.

Idan muka juya zuwa gwamnati kuma, akwai gudunmuwa ta musamman da gwamnati ke ba mu, misali bayanin da yayi a baya cikin hirar, ya bayyana mana irin gyaran da akayi ma sakatariya da tafiya wata jiha cikin jahohin kudu duk gwamnati ta dauki nauyin wannan tafiya, saboda haka akwai kyakyawar alaka da mu kai har da jami’an tsaro babu wata musgunawa da mu ke fuskanta da su musamman ga Dan jarida na kirki.

Akwai kuma bukatar da mu ke da it a ga gwamnati idan Allah yasa mun samu ta gina gidajen Yan jarida da zai ba mu damar zama guru guda dan mai do da martabar zumunci a tsakanin mu, haka mu ma zai ba mu damar sannin junan mu.

Shugaban wanda kuma daraktane a gidan radio na jiha ya kara tabbatar cewa kungiyar zata hada gwuiwa da qungiyar yada labarai ta saman yanar gizo mai lasi za’a jawo su kusa da tsabtace aikin su musamman idan gwamnati ta amince da su.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: