Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Jajircewa – An bawa Abba Kyari sarauta a Yobe

Jami in ɗan sanda a Najeriya DCP Abba Kyari ya samu sarautar Zannah Nduaman  Gujba da ke jihar Yobe.

Abba Kyari ya wallafa a shafinsa na Facebook cewar zai sanar da ranar bikin naɗin sarautar tasa ba da daɗewa ba.

Sarkin Gujba Dakta Mucktar Ibn Ali Gangarang ne ya amince da naɗin sarautar cikin wata takarda da aka aike ga jami in ɗan sandan.

Abba kyari dai jami in ɗan sanda ne mai kwazo tare da hazaƙa a kan aikin sa, kuma ya samu nasarar kama manyan masu aikata laifuka a jihohi daban daban na ƙasar nan.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: