Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Auren Buhari – A karon farko minista Sadiya Umar Farouƙ ta magantu kan lamarin

Kamar yadda a baya aka samu labarin da bai ingnta ba auren shugaban ƙasa Buhari da minista Sadiya Umar Farouƙ, a karon farko ta bayyana cewar ita sam abin bai ɗaɗata da ƙasa ba.

Cikin wata hira da ta yi da jaridar Daily Trust cikin harshen Hausa, Sadiya ta ce a lokacin da ta ji labarin ta san ba gaskiya bane kuma ta gamsu da cewar zai zo ya wuce.

Ta cigaba da cewa ta yarda da kanta kuma ita ba ma abociyar shiga lamuran da ba nata ba, a cewarta ta fi son ta taimaki na ƙasa da ita.

“Har yanzu ba mu haɗu da uwar gidan shugaba Buhari ba wato A isha Buhari saboda aiki da yamin yawa kuma itama nata sun isheta, amma babu wani abu a tsakaninmu na rashin fahimta” inji Sadiya.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya aka kama wani mai suna Kabiru ɗan jihar Kano wanda ake zargi shi ya ƙirƙiri labarin auren Shugaba Buhari da Minista Sadiya Farouƙ.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: