Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ranar rediyo ta duniya – Koma bayan da ake samu a cikin aikin – Mujallar Matashiya

Ranar Rediyo ta duniya, ƙalubalen da ke tattare a ciki
Da sunan Allah mai Rahma Mai jin Ƙai.
Kamar yadda majalisar ɗinkin Duniya ta ware wannan rana da makamanciyarta a matsayin ranar tunawa da rediyo a duniya, zan ɗan yi tsokaci a matsayina na wanda ya ɗan taɓa aikin rediyo kuma nake cuɗanya da ma aikatan a yanzu.
Kowacce shekara ana karkata a kan alfanun rediyo ba tare da duba irin hatsarin da ma aika ko aikin ke fuskanta ba.
Idan muka ɗauki Najeriya ƙasa ce da rediyo ke da matuƙar tasiri tun kafin bayyanar kafafen yanar gizo da a yanzu suke kan gaba wajen saurin isar da saƙo, babu shakka akwai ƙalubale mai tarin yawa da ke tattare a aiki rediyo musamman a yankin arewa.
Zan buga misali da abubuwan da ke faruwa a Kano, mafi yawa a yanzu ana aikin rediyo domin samun suna ko ɗaukaka ko kuma cimma wani buri ba tare da tunanin cewar akwai miliyoyin mutane da ke sauraron kafar ba, ko da yake ana alaƙanta hakan da rashin wadataccen albashi ko rashin albashin ma kamar yadda wasu kafafen ke bawa ma aikata dama don yin aikin ba tare da basu albashi ba, wannan ma na da nasa illar domin hakan ta sa ma aikatan ba sa kallon aikin sai makomarsu, ko da yake akwai masu rashin godiyar Allah.
Misalin wasu shirye-shirye da ake yi a gidajen rediyo akwai kalmomi da rahonnin da basu dace a yaɗa ba saboda irin illar da hakan zai haifar, mun yarda cewa rediyo hanya ce ta isar da saƙo amma wanda zai amfani al umma, idan muka kalli irin rahotannin da ake kawowa musamman na masu aikata ta addanci ko wani aiki na ashsha za mu ga yadda ake rige rigen kawowa al umma ba tare da kawo hukunci ko makomar da mutanen suka kasance ba.
Da yawan wasu ayyukan ana saninsu ne ta hanyar rediyo wanda hakan ka iya zama koma baya ga al umma ganin rashin yaɗuwar hakan a baya.
Mun sani cewar an yadda da labaran da ake sauraro a rediyo kuma idan ma aikatan suka kasance masu kawo sakamakon masu aikata abinda ya haramta walau a dokar ƙasa ko addini na tabbata laifuka za su ragu saboda mutane za su ji tsoron aikatawa.
Ko da yake akwai rashin kwarewa ta wasu ma aikatan yayinda wasu ma ba a fannin suke ba sai alfarma ko kuma son zuciya na rashin saka wanda ya dace ko cancanta sai son zuciya.
A yanzu dai wasu da dama sun ɗauki aikin rediyo a matsayin hanya ta birgewa ba tare da kallon irin nauyin da yake ciki ba, na tafiyar da tarbiyyar al umma da ma rayuwarsu baki ɗaya.
Akwai buƙatar mahukunta su kalli waɗannan matsaloli duk da cewa ƴan ƙalilan na faɗa a kan abubuwan da ke faruwa wanda duk wani ma aikaci a rediyo zai gamsu da haka.
Allah ya sa mu gane kuma mu gyara, ina alfahari da rediyo, ina taya kowa da kowa murnar ranar rediyo ta duniya.
©️Abubakar Murtala Ibrahim
13/2/2020

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: