Shugaban hukumar yaƙi da masu yiwa ƙasa zagon ƙasa EFCC Ibrahim Magu ya bayyana takaici kan yadda ma aikata a Najeriya ke zuwa aiki a makare.

Magu ya ce hakan ma rashawa ne kuma abu ne da za a tashi tsaye domin yaƙarsa.
Ibrahim Magu ya bayyana hakan ne a yayin wani gangami da aka gudanar a Abuja tare da haɗin gwiwar ƴan hidimar ƙasa

Ya ce abin takaici ne a Najeriya ka ga ma aikacin gwamnatin tarayya zai ke wajen aiki da ƙarfe 10:30am na safe.

Ya ce wajibi ne a yaƙi hakan domin babban laifi ne kuma zagon ƙasa ne ga ƙasa.