Tsohon jarumi a masana antar Kannywood Adam Zango ya bayyana cewar ba zai samu damar shiga Kano ba don ganawa da maaoyansa wajen kallom fim ɗin Mati A Zazzau.

Adamu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Kannywood Exclusive wanda ya alaƙanta hakan da siyasa.

Ya ce babu shakka yana matuƙar ƙaunar mutanen Kano duk da cewa a baya ya bayyana ficewarsa daga masana antar amma bai furta cewar ba ruwansa da mutanen Kano ba.

Adam Zango yayi zatrgin wasu a masana antar da ma hukumar tace fina finai da hannu cikin abinda ya ce ” ƙiyayya ce kuma ban san dalilin yimin hakan ba saboda bani da aibi a idonsu”.

A nasa ɓangasren shugaban hukumar tace fina finai da Ɗab i ta jihar Kano Isma ila Na abba Afakallahu ya ce duk mutumin da bai mutunta hukumar ba to bai mutunta jama ar Kano ba kuma za su ladabtar da ahi matuƙar ya karya dokar da suka gindaya.

“Kannywood ita ta yi wa Adam Zango komai, ko saninsa da aka yi dalilinta ne, kuma ahi yasamu masana antar don haka ba za mu kyale duk wanda ya ƙi mutunta sana ar ba”.

Leave a Reply

%d bloggers like this: