Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya karyata rade-radin cewa ya tsallake rijiya da baya a yayin da wasu mahara suka kai farmaki a kan hanyar tashar jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja.

A cewarsa Mun dai ji cewa wasu mahara sun kai farmaki a kan hanyar tashar jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja
Inda ya tabbatar da cewa babu yan bindiga ko masu garkuwa da mutane da suka kai masa hari.

Ministan ya Musanta zargin ne inda Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Ba wanda ya kai min hari, ban ga wasu mahara, yan bindiga ko masu garkuwa da mutane ba kuma ban tsallake rijiya da baya ba, ban tsere ba..”

An dai rawaito cewa Ministan sufuri ya tsallake rijiya da baya a lokacin da mahara suka Kai masa Hari a Jirgin Kasa a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
lamarin ya faru ne da daren Lahadi, 16 ga watan Feburairu,jim kadan bayan jirgin ya sauke fasinjojinsa, inda yawancinsu suka kama sabuwar hanyar da ta tashi daga Rigasa zuwa Mando, daga cikinsu har da ministan sufuri, Rotimi Amaechi.