Kwamishinan yan sandan jihar kano CP Habu Sani Ahmadu ne ya bayyana hakan a wurin Bitar kwana daya da Nigerian Policing Programme ta shirya da hadin gwiwar Rundunar yan sandan jihar kano kan batun tsaftace hanyoyin amfani da kafafen sada zumunta na zamani.

Kwamishinan ya bayyana cewa Rundunar yansandan jihar kano na Kokarin wayar da kan masu amfani da kafafen ta hanyar sanin Ka’dojin da suka hallata ba tare da cin zarafin wani ba ko kuma batanci a gareshi.

Ya kuma kara da cewa wannan kungiyar ta Nigerian Policing Programme ta na taimakawa Yansanda don yada manufofin ta na wayar da kan masu Amfani da kafafen ba tare da batanci ga kowa ba.

Daga karshe CP Habu Sani yayi kira da Wanda suka halarci wurin taron wajen Samar da zaman lafiya a jihar kano.

Taron dai ya samu halartar Masu amfani da kafafen sada zumunta da dama a jihar kano.
Ciki harda Shugaban Mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim.

Daga cikin Wanda suka gabatar da jawabai kan Yadda za’a yi amfani da kafafen sada zumunta ciki harda masana a wannan fage Da suka hada Da Bashir Sharfadi sai kuma jami’an yansanda ASP Yusuf Isa
Da ASP Adamu M Muhammad.
Da kakakin Rundunar yansandan jihar kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: