An samu yara uku ne a jihar Legas a watan Janairun shekarar 2020 da muke ciki.

Kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa kan ɓatan yara a Kano ya tabbatar da sake ceto yara uku da aka kai jihar Legas.
Justice Wada Umar Rano shugaban kwamitin ne ya bayyana hakan yayin da yake gatar da kundin bayanan da suka tattara wanda ya ƙunshi hujjoji kan ɓatan yara a Kano.

Ya ce tun tuni suka miƙa yaran ga iyayensu tare da zaƙulo wata mata da ake zargin tana da hannu wajen satar yara a Kano.

A jawabinsa gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce ɓatan yaran ba zai kalli ƙabila ko yare ba illa yaran jihar Kano a dunƙule.
Sannan ya yaba da ƙoƙarin da kwamitin yayi don ganin ya kammala aikinsa tare da gabatar da rahoton nasarar da ya samu.