Babbar kotun jihar kano karkashin Mai shari’a A T Badamasi a Ranar juma’a ta yanke wa wata Mata hukuncin kisa ta hanyar Rataya.

Kotun dai kama matar Mai Suna Rashida Sai’du da Laifin Kashe mijinta ta hanyar Jefo shi daga saman Bene a lokacin da yake waya.
Rashida ta cefo mijinta Mal Adamu Ali mai shekaru 53 Wanda ya kasance Malami ne a Kwalejin Ilimi ta Tarayya ne daga saman Bene bayan zargin da takeyi na cewa yana yin waya da mace ne.

Lamarin ya faru ne tun A Ranar 25 ga watan Fabrairu 2019 da misalin Karfe 8:00 na dare.

An dai yanke Mata hukuncin ne karkashin sashi na 221 na kundin Penal code