An haramta barar a yau sannan za ta ɗauki matakin shari’a ga iyayen da suka bijirewa dokar.

Hakan ya zo ne bayan wani shiri da mujallar Matashiya ta yi a kan bara da yara ƙanana ke yi a jihar.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya tabbatar da hakan yayin da ake bikin ƙaddamar da sabon tsarin karatun allo da na islamiyya na zamani a garin.

Ganduje ya ce tsarin ilimi kyauta kuma dole a jihar almajirai ma za su amfana da shi kuma wajibi ne ga duk wani ɗan jihar.

Cikin sanarwar da babban sakataren watsa labaran gwamnan Kano Abba Anwar ya fitar, ya ce gwamnati za ta ɗauki matakin shari’a ga iyayen da suka bijirewa dokar.
Tsarin karantarwar zai fara ba da daɗewa ba yayin da aka ɗauki malamai da za su koyar fiye da dubu bakwai.
Batun almajiranci dai lamari ne da ake ta cece kuce a kansa wanda mutane da dama ke sukar lamarin ganin yadda ake kai yara ƙanana bara da sunan karatun allo.
Ko da a baya bayan nan Mujallar Matashiya ta tattauna da manyan mutane biyu a jihar Kano kan lamarin, wanda ake tunani shi ne ya sa gwamnatin fara ɗaukar wannan mataki a farko.